Dec 01, 2018 05:22 UTC
  • Kungiyoyin EU Da ECOWAS Sun Bayyana Damuwarsu Kan Zafafa Hare-Haren Boko Haram

Kungiyar Tarayyar Turai (EU) da kuma kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS sun bayyana tsananin damuwarsu dangane da yadda kungiyar ta'addancin nan ta Boko Haram take kara zafafa hare-haren da take kai wa yankunan arewa maso gabashin Nijeriya.

Kungiyoyin biyu sun bayyana hakan ne cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa da suka fitar a karshen taron hadin gwiwa na kungiyoyin biyu karo na 22 da aka gudanar jiya Juma'a a birnin Abuja, babban birnin tarayyar Nijeriya inda suka jinjinawa irin nasarorin da aka samu a fadar da ake yi da kungiyar ta Boko Haram, to sai dai sun bayyana damuwarsu dangane da irin munanan hare-haren da 'yan kungiyar suke kai wa Nijeriyan cikin 'yan kwanakin nan.

Sanarwar ta kara da cewa kungiyar Tarayyar Turai din ta kara jaddada aniyarta ta ci gaba da goyon baya da kuma karfafa kasashen tafkin Chadi a fadar da suke yi da ayyukan ta'addancin kungiyar ta Boko Haram, bugu da kari kan matsalolin 'yan gudun hijira da ake fuskanta a yankuna Arewa Maso Gabashin Nijeriya din sakamakon rikicin na Boko Haram.

Taron na kungiyoyi biyun dai yana zuwa ne a daidai lokacin da cikin 'yan kwanakin nan kungiyar ta Boko Haram ta zafafa irin hare-haren da take kai wa sansanonin sojin Nijeriya a jihar Borno, musamman harin da suka kai sansanin sojin Nijeriya din da ke garin Metele na jihar Bornon lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar wani adadi na sojojin Nijeriya din.

 

Tags