Nov 29, 2018 17:46 UTC
  • Rundunar Sojin Nijeriya Ta Ce Sojoji 23 Ne Aka Kashe A Harin Metele Ba 100 Da Wani Abu Ba

Rundunar sojin Nijeriya ta bayyana cewar sojoji 23 ne aka kashe a harin da 'yan Boko Haram suka kai wani sansanin sojojinta da ke gariin Metele na jihar Borno ranar 18 ga watan Nuwamba nan sabanin wasu rahotanni da suke cewa sama da sojoji 100 ne aka kashe yayin harin.

Rundunar sojin ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da Birgediya Janar Sani Kukasheka Usman ya fitar a madadin babban hafsan hafsoshin sojan kasa na Nijeriya din Laftanal Janar Tukur Burutai inda sanarwar ta ce sojoji 23 ne aka kashe a yayin harin kana wasu 31 kuma suka jikkata inda tuni aka kai su asibitoci daban-daban a jihar Bornon don ci gaba da jiyya.

Har ila yau Janar Kukasheka ya sake jaddada aniyar rundunar sojin Nijeriyan za ta ci gaba da karfafa sojojin nata masu fada da kungiyar Boko Haram din har sai an cimma aikin da aka sa a gaba na kawo karshen kungiyar da ayyukan ta'addancin da take yi.

Wannan ne dai shi ne karon farko da rundunar sojan ta Nijeriya ta bayyana yawan sojojin da aka kashe a harin na Metele. Kafin hakan dai kafafen watsa labarai da dama sun ta yada wasu bayanai da suke nuni da cewa sama da sojoji 100 ne aka kashe a yayin harin.

A jiya ne dai shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya tafi jihar Bornon don halartar taron babban hafsan hafsoshin Nijeriya da aka gudanar a can don karfafa gwiwan sojojin a fadar da suke yi da 'yan Boko Haram din.

Tags