Ganawar Zarif Da Shugaban Kasar Bolivia
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i10218-ganawar_zarif_da_shugaban_kasar_bolivia
Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zrif ya gana da shugaban kasar Bolivia Evo Morales a birnin Sucre fadar mulkin kasar.
(last modified 2018-08-22T11:28:50+00:00 )
Aug 27, 2016 10:59 UTC
  • Ganawar Zarif Da Shugaban Kasar Bolivia

Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zrif ya gana da shugaban kasar Bolivia Evo Morales a birnin Sucre fadar mulkin kasar.

A lokacin da suke gudanar da tattaunawar a daren jiya, bangarorin biyu sun tabo muhimman batutuwa da suka shafi  alaka a tsakanin kasashen Iran da Volivia, musamman ma a bangarorin harkokin tattalin arziki da cinikayya.

Shugaban kasar Bolivia Evo Morales ya mika wata lambar ban girma ta kasar ga Muhammad Jawad Zarif, tare da halartar manyan jami'an gwamnatin kasar ta Bolivia da suka hada da ministoci da kuma shugaban majalisar dokokin kasar.