Ayatullah Jannati Yayin Hudubar Sallar Juma'a: Al-Sa'ud Jikokin Abu Sufyan Ne
Ayatullah Ahmad Jannati, wanda ya jagorancin sallar Juma'ar birnin Tehran a yau din, yayi kakkausar suka ga halaye da dabi'un mahukutan Saudiyya a yankin Gabas ta tsakiya yana mai siffanta su da cewa su din nan "jikokin Abu Sufyan" ne.
Kamfanin dillancin labaran Fars na Iran ya bayyana cewar Ayatullah Jannatin ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da hudubar sallar juma'a a masallacin Juma'a na Tehran inda yayin da yake ishara da abin da ya faru da alhazai a Mina a shekarar da ta gabata ya bayyana cewar alhazan sun yi shahada ne alhali suna cikin ibada kana kuma sanye da tufafin harami.
Har ila yau yayin da yake magana kan irin halin da alhazan suka rasa rayukansu da kuma gazawar da mahukuntan Saudiyya suka yi wajen ba su kariya, Ayatullah Jannati yayi Allah wadai da irin shiru da halin ko in kula da wasu kasashen musulmi suka nuna kan wannan lamari da kashe sama da alhazan 7000.
Har ila yau kuma yayin da yake magana kan akidar wahabiyanci da gwamnatin Saudiyya take yadawa wanda kuma shi ne tushen irin halin rashin tsaro da ta'addancin da duniyar musulmi take fuskanta a halin yanzu, na'ibin limamin juma'ar na Tehran ya yi ishara da maganar marigayi Imam Khumaini (r.a) inda ya siffanta wahabiyanci a matsayin wani makamin da (makiya) suka yi amfani da shi wajen cutar da musulmi a boye.
A wani bangare na hudubar tasa, Ayatullah Jannati ya jinjinawa wa sakon da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya aika wa maniyyatan banan inda ya ce siffofin da Jagoran ya siffanta mahukuntan Saudiyya da su da suka hada lalatattun mutane, marasa imani, kana masu kirkira da goyon bayan 'yan ta'adda a matsayin wasu siffofi da suka dace da su, yana mai siffanta Al Saud a matsayin jikokin Abu Jahal da Abu Sufyan da kuma Abu Lahab wadanda suka mamaye wajaje masu tsarki na musulmi..