An Fara Gudanar Da Bukukuwan Tunawa Da Kallafaffen Yaki A Iran
Bangarori daban-daban na sojojin Iran sun gudanar da gagarumin fareti da gwajin nau'oi daban-daban na makamai a ranar farko na bukukuwan Makon Kariyar don tunawa da zagayowar shekaru 36 da zagayowar kallafaffen yaki na shekaru takwas da tsohuwar gwamnatin Iraki ta kallafawa Iran.
Kamfanin dillancin labaran Iran IRNA ya bayyana cewar an gudanar da babban taron ne a kusa da hubbaren marigayi Imam Khumaini (r.a) da ke birnin Tehran inda dakarun kasar Iran din da suka hada da sojoji, dakarun kare juyin juya halin Musulunci da kuma 'yan sandan kasar suka gudanar da fareti da kuma gwada wasu daga cikin makaman da suke da shi.
A yayin bikin na bana dai sojojin na Iran sun gwada sabbin makaman kariya da suka kera da suka hada nau'oi daban-daban na makamai masu linzami da kuma na'urori na kariya. Har ila yau kuma dakarun na Iran sun gwada sabuwar na'urar kariyar nan ta S-300 da kuma makami mai linzamin nan na Emad wanda dakarun suka gwada shi a watan Oktoban shekarar da ta gabata wanda ya janyo hankulan duniya.
Baya ga birnin Tehran din har ila yau kuma an gudanar da irin wadannan bukukuwan a wasu garuruwa na daban na Iran din