Ayatullah Kermani: Babu Bukatar Damfara Fata Da Amurka
Wanda ya jagoranci sallar Juma'ar birnin Tehran kuma memba a majalisar kwararru ta jagoranci ta Iran Ayatullah Muhammad Ali Muwahhidi Kermani ya bayyana cewar babu wata bukata ta damfara fata da Amurka don kuwa ita ba abar yarda ba ce.
Ayatullah Muhammad Ali Muwahhidi Kerman ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da hudubar sallar Juma'a a nan Tehran inda yayi kakkausar suka ga wadanda suke kiran da a yi kokarin tafiya tare da Amurka.
Ayatullah Kermani ya kara da cewa babu wani abin da Amurka ta ke yi wanda zai amfani Iran face dai abubuwan da za su cutar da ita da kuma al'ummar kasar don haka yayi kiran da a kara himma wajen ciyar da kasar Iran gaba da kuma dogaro da irin karfi na cikin gida da ake da shi.
A wani bangare na hudubar tasa, wanda ya jagoranci sallar Juma'ar na Tehran ya sake jaddada maganganun da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya yi na wajibcin aiwatar da siyasar tattalin arziki na dogaro da kai wanda ya ce hakan ne kawai hanya guda da Iran za ta samu karfaffen yanayi na tattalin arziki da kuma kare kanta daga duk wata barazana ta makiya a wannan bangaren.