Jagora: Makircin Makiya A Kan Iran Ya Zama Aikin Baban Giwa
(last modified Wed, 24 Feb 2016 11:10:17 GMT )
Feb 24, 2016 11:10 UTC
  • Jagora: Makircin Makiya A Kan Iran Ya Zama Aikin Baban Giwa

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar makirce-makicen makiya na hana al'ummar mika mubaya'arsu ga tsarin Musulunci na kasar tsawon shekaru 37 din da suka gabata ya zama aikin baban giwa.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi dazu da safe da mutanen garin Najafabad da suka kai masa ziyarara inda yayin da yake magana kan zaben 'yan majalisar shawarar Musulunci da ta kwararru ta jagoranci ya bayyana cewar ko shakka babu al'ummar Iran za su zabi 'yan majalisar da za su yi tsayin daka ne wajen tinkarar tsoma bakin 'yan kasashen waje wadanda kuma ba sa tsoron Amurka.

Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar tun bayan yarjejeniyar nukiliya da aka cimma tsakanin Iran da manyan kasashen duniya, ma'abota girman kai musamman Amurka suke kokari wajen haifar da rarrabuwan kai tsakanin al'ummar Iran, sai dai ya ce ko shakka babu makiyan ba za su cimma wannan manufa ta su ba.

Ayatullah Khamenei dai ya ce al'ummar Iran suna son kafa majalisa ce wacce za ta damu da matsalolin mutane sannan kuma wacce za ta tsaya kyam wajen tinkarar masu kokarin tsoma baki cikin harkokin cikin gidan Iran.