Shamkhany: Sake Kakaba Takunkumi, Keta Yarjejeniyar Nukiliya ce.
(last modified Wed, 16 Nov 2016 06:56:47 GMT )
Nov 16, 2016 06:56 UTC
  • Shamkhany: Sake Kakaba Takunkumi, Keta Yarjejeniyar Nukiliya ce.

Kin amincewar Iran da sake kakabawa Iran takunkumi

Babban Sakataren Majalisar Koli Ta Tsaron Kasar Iran, Ali Shamkhany,  ya bayyana cewa; Matukar aka keta yarjejeniyar Nukiliya to Iran za ta bada jawabi cikin sauri.

Bugu da kari, Ali Shamkhany ya ce; Masu sanya idanu na kasa da kasa da kasashen sun tabbatar da ingancin aiwatar da yarjejeniyar, domin haka keta da daya gefen zai yi, zai rusa ta.

Babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar, ya kuma ce; A wurin jamhuriyar musulunci ta Iran wacce ta ginu a bisa tsarin juyin juya hali tana fada da masu nuna girman kai, babu wani abu da zai faru don an sami sauyin jagoranci a wata kasa.

Da ya ke magana akan ziyarar 40 ta shahadar Imam Hussain, Ali Shamkhany ya ce; taron yana a matsayin girman musulunci ne kuma zai iya samar da wata dama ta siyasa da zamantakewa da gina kyawawan al'adu a cikin duniyar musulunci.