Martanin Sojan Ruwa Na Dakarun Kare Juyin Musulunci Ga Shisshigin Amurka.
(last modified Wed, 30 Nov 2016 06:18:50 GMT )
Nov 30, 2016 06:18 UTC
  • Martanin Sojan Ruwa Na Dakarun Kare Juyin Musulunci Ga Shisshigin Amurka.

Dakarun Kare Juyin Musulunci Sun Maida Martani Ga Amurka

Wani jami'in dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran, ya bayyana cewa; Tushen matsala a wannan yankin shi ne girke sojojin da Amurka ta yi a tekn pasha.

Majiyar labaru ta dakarun kare juyin musulunci, ta ambaton  jami'in yana maida martani akan bayanin ma'aikatar tsaron Amurka na cewa dakarun kare juyin juya halin musulunci sun kai wa jirgi mai saukar angulu na Amurka hari a mashigar Hurmuz, sannan ya jaddada cewa: Tushen matsalar da ake fuskanta a tekun pasha ita ce, zuwan sojojin Amurka a cikin yanki ba tare da wani dalili ba.

Majiyar dakarun kare juyin musuluncin ta ci gaba da cewa; Abinda Amurkawa su ka sa a  gaba shi ne parpaganda domin cimma manufofinsu.

Wani sashe na bayanin dakarun kare juyin musuluncin ya ci gaba da cewa a dare da rana, jiragen ruwa na kai da komowa ba tare da wata matsala ba, tare da aiki da dokokin kasa da kasa na fito. Amurkawa ne kadai wadanda su ke kwakwazo, saboda kokarin cimma manufofinsu.