Rauhani: Hadin Kai Shi ne Tushen Karfin Al'ummar Musulmi
Shugaban Kasar Iran: Tushen Karfin Musulmi Shi ne Hadin Kai.
Shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ya ce; Tarihin Manzon Allah (s.a.w.a) shi ne abin koyi ga musulmi.
shugaban jamhuriyar musulunci ta Iran, Dr. Hassan Rauhani wanda ya gana da musulmi mabiya mazhabobin sunna anan Iran a ranakun maulundin manzon Allah (s.a.w.a) ya kara da cewa; Kabilu da kuma mazhabobi mabanbanta da ake da su, wara babbar dama ce ta hada kan kasa da kuma ci gaban al'umma, bai kamata a dube su a matsayin barazana ba.
Da ya ke magana akan kungiyoyi masu kafirta musulmi, Dr. Hassan Rauhani ya ce; Ba su da wani aiki da ya wuce bakanta sunan musulunci da musulmi a duniya.
A Iran ana raya bukukuwan Mauludi ne daga ranar 12 ga watan Rabi'ul Auwal zuwa 17 gare shi, bisa banancin riwayoyin haihuwar fiyayyen halitta a tsakanin sunnan da shi'a.