Ministan Tsaron Iran Ya Fara Ziyarar Aiki A Kasar Afirka Ta Kudu
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i15199-ministan_tsaron_iran_ya_fara_ziyarar_aiki_a_kasar_afirka_ta_kudu
Ministan Tasaron Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Husain Dagqan ya isa birnin Pretoria dazu.
(last modified 2018-08-22T11:29:23+00:00 )
Dec 13, 2016 06:20 UTC
  • Ministan Tsaron Iran Ya Fara Ziyarar Aiki A Kasar Afirka Ta Kudu

Ministan Tasaron Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Husain Dagqan ya isa birnin Pretoria dazu.

Ministan Tasaron Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Husain Dagqan ya isa birnin Pretoria  da safiyar yau talata.

Ziyarar ta ministan tsaron jamhuriyar musulunci ta Iran ta zo ne a matsayin amsa kiran takwararsa ta Afirka ta kudu Madam Mapisa Ankakola.

A yayin, ziyarar tashi dai zai gana da manyan jami'an gwamnatin kasar ta Afirka ta kudu domin tattauna hanyoyin bunkasa alaka a tsakanin kasashen biyu.

Haka nan kuma kasashen biyu za su rattaba hannu akan yarjeniyoyi na fahimtar juna akan harkokin tsaro.