Dr.Ali Larijani: Raba Kan Musulmi Shi ne Babban Cin Amana
(last modified Thu, 15 Dec 2016 19:17:28 GMT )
Dec 15, 2016 19:17 UTC
  • Dr.Ali Larijani: Raba Kan Musulmi Shi ne Babban Cin Amana

A cikin kasashen wannan yankin na gabas ta tsakiya da akwai wadanda su ke hada kai da kungiyoyin 'yan ta'adda.

Shugaban Majalisar Shawarar musulunci ta Iran Dr. Ali Larijani ya ce; Babban cin amanar al'ummar musulmi yana tattare da duk wani aiki da ke raba kawunan musulmi.

Dr. Ali Larijani ya ci gaba da cewa; A cikin kasashen wannan yankin na gabas ta tsakiya da akwai wadanda su ke hada kai da kungiyoyin 'yan ta'adda.

 Shugaban majalisar shawarar musuluncin ta Iran ya kuma ce; Kasashen da su ke hada da haramtacciyar kasar Isra'ila domin raba kawunan musulmi, sun jawo kawukansu kaskanci, haka nan kuma masu aiki da yan ta'adda domin tarwatsa hadin kan musulmi.

Dr. Ali Larijani ya ci gaba da cewa; Wajibi ne ga musulmi shi'a da sunna da su fahimci cewa wuce gona da iri ba abinda ya ke jawo wa musulmi illa matsaloli da kuma rabuwa.

Shugaban Majalisar shawarar musulunci ta Iran ya bayyana yadda Iran ta ke da zaman lafiya da kwanciyar hankali duk da cewa a cikin wasu kasashen yankin da akwai kayan aiki na soja da tsaro fiye da Iran.

Jawabin na shugaban majalisar shawarar musulunci ta Iran ya zo ne a wurin girmama shahidan gundumar Gulustan 4000 da safiyar yau alhamis.