Ministan Harkokin Wajen Syria Na Gudanar Da Ziyarar Aiki A Tehran
A yau ne ministan harkokin wajen kasar Syria Walid Mu'allim yake gudanar da wata ziyarar aiki a birnin Tehran, domin ganawa da manyan jami'an gwamnatin kasar Iran.
Ministan harkokin wajen kasar ta Syria ya gana da takwaransa na Iran Muhammad Jawad Zarif, inda suka tattauna muhimamn batutuwa da suka shafi halin da ake cikia a Syria, musamman ta fuskar siyasa.
Bayann kuma Mu'allim ya gana da babban sakataren majalisar tsaron kasa a Iran Admiral Ali Shmakhani, inda suka yi dubi kan shirin tsagaita wuta a Syria, da kuma ci gaba da yin aiki tare da tsakanin Iran da Rasha da kuma Syria, wajen tabbatar da sulhu da zaman lafiya a kasar ta Syria.
Daga karshe Mu'allim ya gana da shugaba Hassan Rauhani, inda ya jinjina wa kasar Iran kan tsayin dakan da ta yi wajen taimaka ma kasar Syria a fagagen da dama, da suka hada da yaki da ta'addanci, da kuma bangaroin siyasa da tattalin arzki da sauransu.
Shi am anasa bangare shugaba Rauhani ya jaddada cewa babu gudu babu ja da baya wajen ci gaba da kare halastacciyar gwamnati a Syria, tare da taimaka mata wajen yaki da 'yan ta'adda.