Harin Ta'addanci A Gundumar Najaf Ta Iraki.
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i15973-harin_ta'addanci_a_gundumar_najaf_ta_iraki.
Mutane da dama ne su ka mutu a wani harin ta'addanci a gundumar Najaf
(last modified 2018-08-22T06:59:28+00:00 )
Jan 01, 2017 08:35 UTC
  • Harin Ta'addanci A Gundumar Najaf Ta Iraki.

Mutane da dama ne su ka mutu a wani harin ta'addanci a gundumar Najaf

Tashar Telbijin din Press tv ta nakalto cewa wata mota da aka makare da bama-bamai ta tashi a yankin Qadisiyya da ke gundumar Najaf. Kawo ya zuwa yanzu an tabbatar da mutuwar mutane 6 da kuma jikkatar wasu fiye da 20.

Wata majiyar tsaro ta ce wadanda harin ya rutsa da su fararen hula ne. Tuni dai aka killace yankin da jami'an tsaro da  kuma daukar wadanda su ka jikkata zuwa asibiti domin yi musu magani.

Kamfanin dillancin labarun al-sumriyyah, ya sanar da cewa wasu mutane dauke da bindigogi sun kai hari a  yankin al-mushkhab a gunduma ta Najaf. Sai dai kawo ya zuwa yanzu babu bayani akan wadanda su ka jikkata.