Ministan Harkokin Wajen Syria Na Ci Gaba Da Ziyara A Iran
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i15976-ministan_harkokin_wajen_syria_na_ci_gaba_da_ziyara_a_iran
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Ta Iran Ya Gana Da Ministan Harkokin Wajen Kasar Syria da ke ci gaba da ziyara a Iran
(last modified 2018-08-22T06:59:28+00:00 )
Jan 01, 2017 08:35 UTC
  • Ministan Harkokin Wajen Syria Na Ci Gaba Da Ziyara A Iran

Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Ta Iran Ya Gana Da Ministan Harkokin Wajen Kasar Syria da ke ci gaba da ziyara a Iran

Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Ta Iran Ya Gana Da Ministan Harkokin Wajen Kasar Syria da ke ci gaba da ziyara a Iran a yau lahadi.

Dr. Ali  Larijani wanda ya  tattauna da  Walid Mu'allim akan halin da ake ciki a kasar Syria da ya hada da tsagaita wutar yaki, da kuma yadda za a bude tattaunawar sulhu a tsakanin bangaren gwamnati da 'yan adawa.

A jiya asabar ne dai ministan harkokin wajen kasar ta Syria wa'lid Mu'allim ya iso Iran tare da shugaban hukumar tsaron kasar Syria, Mamluk domin musayar ra'ayi da mahukuntan Iran.