Wilayati: Iran Ba Za Ta Watsi Da Gwamnati Da Al'ummar Siriya Ba
Babban mai ba wa Jagoran juyin juya halin Musulunci shawara kan harkokin kasashen waje, Dakta Ali Akbar Wilayati ya bayyana cewar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za taba yin watsi da mutane da kuma gwamnatin kasar Siriya ba.
Dakta Ali Ali Akbar Wilayati ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da mataimakin shugaban kasar Iraki Nouri al-Maliki a ziyarar da ya kawo nan Iran inda ya ce: Ko da wasa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta taba yin watsi da akidarta ta goyon bayan sansanin gwagwarmayar ciki kuwa har da al'umma da kuma gwamnatin kasar Siriya.
Haka nan kuma yayin da yake magana kan shirin sulhu da zaman lafiyan kasar Siriya da ake gudanarwa kuwa, babban mai ba wa Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran din shawarar kan harkokin kasashen wajen ya bayyana cewa dukkanin kokarin da Iran da kasar Rasha suke yi a wannan bangaren, suna yin hakan ne ta hanyar hadin gwiwan da gwamnatin kasar Siriyan, yana mai cewa babu wani ko wata kasa da take da hakkin tsoma baki cikin harkokin cikin gidan Siriya.
A shekaran jiya ne dai mataimakin shugaban kasar Irakin, Nouri Al-Maliki ya kawo ziyarar aiki nan Iran don tattaunawa da manyan jami'an kasar dangane da yanayin da ake ciki a yankin Gabas ta tsakiya ciki kuwa har da rikicin kasar Iraki da Siriyan da kuma fada da ta'addanci da ake yi a wadannan kasashe da nufin kawo karshen kungiyoyin 'yan ta'addan da aka shigo da su wadannan kasashe biyu.