Ali Larijani: Dukkanin Mabiya Addinai Suna Da 'Yanci A Iran.
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Ta Iran ya ce; Dukkanin Mabiya Addinai Suna Da 'Yanci A Karkashin Tsarin Mulki.
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Ta Iran ya ce; Dukkanin Mabiya Addinai Suna Da 'Yanci A Karkashin Tsarin Mulki.
Shugaban Majalisar Shawarar musuluncin ta Iran wanda ya gana da 'yan majalisa masu wakiltar kiristocin Ashur da Armaniyawa, saboda shigowar sabuwar shekarar miliadiyya ta 2017, ya ce; A cikin tsarin mulkin Iran, dukkanin mabiya adddinai suna da hakkoki iri daya.
Ali Larijani ya taya mabiya addinin kiristocin na Iran murnar shigowar sabuwar shekarar miladiyya sannan ya kara da cewa; Annabi Isa (a.s) daidai da sauran annabawa ya zo ne da sakon zaman lafiya da sulhu, sannan kuma ya yi aiki ne domin shimfida adalci da kauna a tsakanin mutane.
A nasu gefen, 'yan majalisa masu wakiltar mabiya addinin kiristanci na Ashurawa da Aramaniyawa, Yunatin But Kulya, da Karin Khanru da GGoegic Abramiyan sun jadda wajabcin ci gaba da kare hadin kan da al'ummar Iran su ke da shi.