Iran: Ma'aikatar harkokin Waje Ta Kirayi Jakadan kasar Switzerland Mai Wakiltar Amurka.
(last modified Sun, 29 Jan 2017 19:10:43 GMT )
Jan 29, 2017 19:10 UTC
  • Iran: Ma'aikatar harkokin Waje Ta Kirayi Jakadan kasar Switzerland Mai Wakiltar Amurka.

Kakakin Ma'aikatar harkokin Wajen Iran ya sanar da kiran jakadan kasar Switzerland domin nuna masa kin amincewar Iran da matakin Shugaban Kasar Amurka na kin jikin 'yan gudun hijira.

Kakakin Ma'aikatar harkokin Wajen Iran ya sanar da kiran jakadan kasar Switzerland  domin nuna masa kin amincewar Iran da matakin Shugaban Kasar Amurka na kin jikin 'yan gudun hijira.

Bahram Kasimy y aci gaba da cewa; An gabatarwa da jakadan kasar ta Switzerland takardar kin amincewa ne da dokar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi, na hana yan kasar Iran shiga kasar tare da bayyana hakan a matsayin nuna wariya.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen na Iran ya ci gaba da cewa; Dalilin da Amurkan ta bijiro da shi, ba shi da madogara, kuma yana cin karo da dokokin kare hakkin bil'adama na kasa da kasa.

Shugaban Amurka Donald Trump ya rattaba hannu akan dokar hana yan kasashen bakwai na musulmi shiga cikin kasar ta Amurka, Kasashen sune; Iran da Iraki da Sudan da Somaliya da Libya da Syria da Yemen.