Dr. Hassan Rauhani: Babu wani Makami da ya fi Azama, karfi.
Shugaban Kasar Iran Dr. Hassan Rauhani ya ce; Babu wani Makami da ya fi imani da gwagwarmaya da hadin kan al'umma karfi
Shugaban Kasar Iran Dr. Hassan Rauhani ya ce; Babu wani Makami da ya fi imani da gwagwarmaya da hadin kan al'umma karfi.
Shugaban kasar na Iran wanda ya ke gabatar da jawabi a wurin taron girmama shahidai na duniyar musulunci, a garin Mashhad da ke arewa maso gabacin Iran ya kara da cewa: Matasan Iran a tsawon shekaru 8 na yakin tsaron kasa, sun sami nasara ne saboda karfin azamarsu, haka nan Hizbullah a kasar Lebanon a yakin da su ka yi da haramtacciyar Kasar Isra'ila.
Shugaban kasar na Iran ya kara da cewa; A kasar Iraki ma al'umma sun sami nasara akan 'yan ta'adda saboda azamar da su ke da su.
A kasar Yemen ma azama ta sami fifiko da nasara akan makamai na zamani da kasashen da su ke yakin kasar su ke da su.
Iyalan shahidai daga kasashen musulmi da dama suna halartar taron na Iran. Sun kunshi Iraki, Lebanon, Syria, Pakistan,Tunisiya da kuma Bosnia.