Iran: Majalisar Dinkin Duniya Ta Zama Dandalin Wasan Kwaikwayo
Shugaban cibiyar kare hakkin bil'adama ta Iran ya ce; Majalisar Dinkin Duniyar wani filin wasan kwaikwayo ne da Amurka ta ke a matsayin 'yar wasa.
Shugaban cibiyar kare hakkin bil'adama ta Iran ya ce; Majalisar Dinkin Duniyar wani filin wasan kwaikwayo ne da Amurka ta ke a matsayin 'yar wasa.
Muhammad Jawad Larijani ya yi ishara da dubban kananan yaran da 'yan koren Saudiyya su ke kashe wa a cikin kasar Yemen, sannan ya kare da cewa, yakin da ake yi da Yemen ne abinda ya jaza, mutuwar kananan yaran.
Har ila yau, larijani ya ce; Yin magana akan kare hakkin bil'adama ba tare da la'akari da tsarin demokradiyya ba, ba abu ne mai yiyuwa ba,sannan ya kara da cewa; Jamhuriyar musulunci ta Iran, ita ce ginshikin tsarin demokradiyya a cikin wannan yankin, amma cibiyar kare hakkin bil'adama da ta ke karkashin ikon Amurka, tana sanya alamar tambaya akan hakan.