Iran Ta Mayar Da Martani Da Zarge-Zarge 'Maras Tushe' Na Turkiyya
(last modified Mon, 27 Mar 2017 05:46:10 GMT )
Mar 27, 2017 05:46 UTC
  • Iran Ta Mayar Da Martani Da Zarge-Zarge 'Maras Tushe' Na Turkiyya

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi watsi da tuhumce-tuhumce "marasa tushe" da shugaban kasar Turkiyya Rajab Tayyip Erdogan yayi mata tana mai cewa Turkiyya tana zargin wasu kasashe na daban ne don ta rufe da kuma halalta bakar siyasarta ta neman mulkan sauran al'umma.

Kakakin Ma'aikatar harkokin wajen Iran Bahram Qassemi ne ya bayyana hakan yayin da yake mayar da martani kan kalaman shugaba Erdogan na Turkiyyan inda ya ce jami'an kasar Turkiyya suna kokarin halalta irin baki cikin harkokin wasu kasashe da suke yi da kuma siyasarsu ta mulkin mallaka ne ta hanyar ci gaba da zargin wasu kasashe na daban.

Har ila yau kakakin Ma'aikatar harkokin wajen na Iran ya kirayi jami'an kasar Turkiyya da su guji irin wadannan tuhumce-tuhumce marasa tushe kana kuma su yi kokari wajen girmama mutumci da ikon da kasashe da suke makwabtaka da su musamman kasashen Iraki da Siriya inda Turkiyya take ci gaba da taka gagarumar rawa wajen dagula lamurran tsaro a wadannan kasashe ta hanyar taimakon kungiyoyin 'yan ta'addan da suke yaki a can.

A shekaran jiya Asabar ne dai shugaban kasar Turkiyyan, a yayin wani jawabi da yayi a garin Antalya da ke kudancin Turkiyya ya zargi Iran da gudanar da siyasar wariya a kasar Iraki. Erdogan yana wannan maganar ne a daidai lokacin da gwamnatin Iraki take zargin gwamnatinsa da aikata irin wannan siyasar a kasar da kuma taimakon 'yan ta'addan a kasar Irakin.