Iran Ta Yi Allah Wadai Da Harin Amurka A Syria
Jamhuriya Musulinci ta Iran ta ty Allah wadai da kakkausar murya kan harin da Amuirka ta kaiwa sansanin sojin Syria a cikin daren Jiya.
Gidan talabijin din Press TV na Iran na ya nakalto gwamnatin Iran na cewa harin da Amurka ta kai a sansanin sojin na Syria abun takaici ne kasancewar ana cikin bincike domin gano hakikakin wa keda hannu a harin makami mai guda da aka kai a Syria.
A halin da ake ciki dai kasar Rasha ta kira wani taron gaggawa na kwamitin tsaro MDD biyo bayan harin makamai masu linzami da Amurka ta kai sansanin sojin dake tsakiyar kasar ta Syria.
Harin da AMurka ta kai Syria na zuwa ne a yayin da gwamnatin Shugaban Bashar Al'Asad ta bayyana a jiya cewa ana nuna goyon baya ga kasa da kasa da su kafa kwamitin yin bincike kan batun yin amfani da makamai masu guba a jihar Idlib.
Ministan harkokin wajen kasar Walid Muallem, ya bayyana cewa, kasarsa tana nuna goyon baya ga kasa da kasa da su kafa kwamitin yin bincike kan batun yin amfani da makamai masu guba a jihar Idlib dake arewa maso yammacin kasar, amma ya kamata a magance yin amfani da kwamitin wajen cimma manufofin siyasa.