An Fara Fara Rajistar 'Yan Takara A Zaben Shugaban Kasar Iran
A Safiyar Yau Talata ce aka fara rajistan 'yan takara a zaben Shugaban kasar Iran karo na 12 a cibiyoyin zaben kasar
Kamfanin dillancin labaran Irna na kasar Iran ya habarta cewa a safiyar yau Talata ce aka fara rajistan 'yan takarar Shugabancin kasar karo na 12, wanda za a ci gaba da yi har zuwa kwanaki biyar masu zuwa wato zuwa ranar Assabar 15 ga watan Favrayu.
Bisa doka mai lamba 115 na kundin tsarin milkin kasar Iran da kuma doka mai 35 na kundin tsarin zaben kasar ya baiwa 'yan siyasar da suka cika sharuda masu kuma son tsayawa takarar Shugaban kasar damar komawa zuwa ga cibiyar hukumar da ke ma'aikatar harkokin cikin gida don rajistar sunayensu. daga cikin wadannan sharudan tsayawa takarar Shugabancin kasar .yashi ne kasancewa Namiji , mai riko da Addini, kuma Dan kasar Iran, yana kyakkyawan suna da kuma kwarewa a mikaman da ya rike a baya, Mumini, mai tsoron Allah da kuma imani da tsarin Jumhoriyar musulinci ta Iran.
A ranar 19 ga watan Mayu 2017 mai kamawa ne dai za a gudanar da zaben shugaban kasa karo na 12 da kuma zabububbukan majalisun kananan hukumomi karo na biyar a duk fadin kasar Iran.