Ministan Cikin Gidan Iran: Za'a Gudanar Da Zabe Cikin Adalci
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i19352-ministan_cikin_gidan_iran_za'a_gudanar_da_zabe_cikin_adalci
Ministan harkokin cikin gisa na kasar Iran Abdurrida Rahamani Fadli ya bayyana cewa za'a gudanar da zabubbuka a cikin kasar Iran cikin adalci da nutsuwa a duk fadin kadar.
(last modified 2019-08-10T10:24:46+00:00 )
Apr 11, 2017 14:33 UTC
  • Ministan Cikin Gidan Iran: Za'a Gudanar Da Zabe Cikin Adalci

Ministan harkokin cikin gisa na kasar Iran Abdurrida Rahamani Fadli ya bayyana cewa za'a gudanar da zabubbuka a cikin kasar Iran cikin adalci da nutsuwa a duk fadin kadar.

Kamfanin dillancin labaran IRNA ya nakalto ministan yana fadar haka a yau Talata jim kadan bayan an fara rijistar yan takara a zaben shugaban kasa da na majalisar jihohin kasar. Ministan ya kuma kara da cewa ma'aikatarsa zata yi aiki tare da majalisar dokokin kasar da kuma majalisar kare kundin tsarin mulkin kasar don ganin an gudanar da zabubbukan cikin kwanciyar hankali da adalci.

Rijistar yan takaran dai, zai dauki kwani ki bayar ana yi, sannan za'a gudanar da zabubbukan ne a ranar 29 ga wata Urdee behesht ko kuma 19 ga watan Mayu na shekaran da muke ciki.