An Fara Aikin Tantance Masu Bukatar Tsayawa Takaran Shugabancin Kasar Iran
Kakakin majalisar kula da kundin tsarin mulki na kasar Iran ya sanar da cewa an fara tantance mutanen da suka yi rajistar sunayensu a matsayin 'yan takaran shugabancin kasar Iran a zaben da za a yi a wata mai kamawa.
Kafar watsa labaran Hukumar Gidan Radiyo Da Talabijin Na Iran ta bayyana cewar a wata ganawa da yayi da manema labarai, Abbas Ali KodKhodayi, kakakin majalisar kula da kundin tsarin mulki na kasar Iran din ya bayyana cewar tuni an fara tantance sunayen 'yan takaran da suka yi rajistar sunayen na su kamar yadda doka ta tanadar yana mai cewa bisa doka din dai hukumar da ke da alhalin tantance 'yan takarar tana da kwanaki biyar ta yi hakan bayan an gama rajistar sunayen 'yan takaran.
Kafin hakan dai shugaban cibiyar zaben Ali Asghar Ahmadi ya ce mutane 1,636 ne suka yi rajistar sunayen na su ciki kuwa har da mata 137 tsawon kwanaki biyar da aka yi ana rajistar wadanda suke son tsayawa takaran shugabancin kasar ta Iran.
A ranar 19 ga watan Mayu mai kamawa ne dai za a gudanar da zaben shugaban kasa karo na 12 a kasar Iran din.