An Shiga Rana Ta Biyu A Gasar Kur'ani Ta Duniya A Tehran
(last modified Thu, 20 Apr 2017 17:48:57 GMT )
Apr 20, 2017 17:48 UTC
  • An Shiga Rana Ta Biyu A Gasar Kur'ani Ta Duniya A Tehran

An shiga rana ta biyu a gasar kur'ani ta duniya da aka bude a jiya a birnin Tehran na kasar Iran a babban dakin taruka da ke babban masalalcin marigayi Imam Khomeni.

Wannan gasa da aka bude a jiya, tana samun halartar makaranta da mahardata kur'ani mai tsarki daga kasashe 82 na duniya, da suka hada da kasashen musulmi da na larabawa, da kuma wasu kasashen nahiyar Afirka da na turai da kuma na asia.

Wannan dai shi ne karo na 34 da ake gudanar da wannan gasa ta duniya a kowace shekara a kasar ta Iran, inda akan dauki mako guda ana gudanar da ita.

Gasar dai ta shafi bangarori na harda da kuma kira'a, kamar yadda kuma a kan tabo bangaren hukunce-hukuncen karatun kur'ani (tajwidi) da kuma tafsiri, inda daga karshen gasar a kan bayar da kyautuka ga dukkanin wadanda suka halarci gasar, da kuma wasu kyautukan na musamman ga wadanda suka fi nuna kwazo.

A wannan karo dai gasar ta dauki wani sabon salo a karon farko, inda ake gudanar da gasar a bangarori uku, bangaren na farko shi ne na makaranta da mahardata kamar yadda aka saba, sai kuma bangare na biyu shi ne bangaren makaranta da mahardata mata, sai kuma bangaren gasar kur'ani ta nakasassu.