A Yau Ne 'Yan Takarar Shugabancin Kasar Iran Suka Gudanar Da Muhawara
Apr 28, 2017 12:29 UTC
'Yan takarar shugabancin kasar Iran sun gudanar da muhawara ta farko a yau, domin bayyana irin tsare-tsaren da kowannesu yake da shi idan ya samu nasarar lashe zabe.
'Yan takarar 6 su ne; Hassan Rauhani, Ibrahim Ra'isi, Mustafa Agha Mirsalim, Muhammad Bakir Qalibaf, Musatafa Hashimi Taba, Ishaq Jihangiri.
Dukkanin 'yan takarar sun gabatar da bayani daidai wa'adin lokacin da aka kayyade musu, tare da amsa tambayoyi a kan shirin nasu.
Wannan dai shi ne karo na 12 da za a gudanar da zaben shugaban kasa a Iran tun bayan samun nasarar juyin juya halin muslunci a cikin shekara ta 1979, zaben shugaban kasar Iran mai zuwa zai gudana ne a ranar 19 ga watan Mayu mai kamawa.
Tags