'Yan Takarar Shugabancin Iran Na Ci Gaba Da Yakin Neman Zabe
May 04, 2017 12:21 UTC
Dukkanin 'yan takarar neman shugabancin kasar Iran a zabe mai zuwa, suna ci gaba da yakin neman zabe.
'Yan takarar guda 6 wato Hassan Rauhani, Ishaq Jihangiri, Muhammad Baqer Qalibaf, Musatafa Agha Mir Salim, Ibrahim Ra'isi, Mustafa Hashimi Taba, a yau sun gabatar da jawabai a tashoshin talabijin daban-daban na kasar Iran.
Dukkanin bayanan nasu suna da alaka ne da irin tsare-tsaren da suke da su a fuskoki daban-daban wajen tafiyar da kasar idan suka samu nasarar lashe zabe.
A gobe ne dukkanin 'yan takarar 6 za su sake haduwa wuri guda domin tafka muhawara gaba da gaba a karo na biyu.
Tags