'Yan Takarar Shugabancin Iran Za Su Gudanar Da Muhawara Ta Biyu
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i20094-'yan_takarar_shugabancin_iran_za_su_gudanar_da_muhawara_ta_biyu
A yammacin yau ne 'yan takaran shugabancin kasar Iran a zaben shugaban kasar da za a gudanar nan gaba su shida za su gudanar da muhawararsu ta biyu wanda gidan talabijin na kasar zai watsa kai tsaye.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
May 05, 2017 05:17 UTC
  •  'Yan Takarar Shugabancin Iran Za Su Gudanar Da Muhawara Ta Biyu

A yammacin yau ne 'yan takaran shugabancin kasar Iran a zaben shugaban kasar da za a gudanar nan gaba su shida za su gudanar da muhawararsu ta biyu wanda gidan talabijin na kasar zai watsa kai tsaye.

A wata sanarwa da kwamitin da ke kula da yakin neman zaben 'yan takaran ya fitar ya ce a yammacin yau Juma'a da misalin karfe 4:30 agogon Iran wato karfe 12:00 na rana agogon GMT ne 'yan takaran za su gudanar da muhawar ta su ta biyu wacce za ta tabo batutuwan da suka shafi siyasa ne.

Muhawarar farko dai wacce aka yi ta a ranar Juma'ar da ta gabata ta ba da muhimmanci ne kan lamurran da suka shafi zamantakewar al'umma inda 'yan takarar suka yi bayanin mahangarsu kan lamarin da kuma yadda za su magance matsalolin da ake fuskanta a wannan bangaren matukar dai aka zabe su a matsayin shugaban kasa.

'Yan takarar guda 6 dai su ne; Hassan Ruhani, Ibrahim Ra'isi, Mustafa Agha Mirsalim, Muhammad Bakir Qalibaf, Musatafa Hashimi Taba da kuma Ishaq Jihangiri wanda ake sa ran za su fafata a zaben da za a gudanar a ranar 19 ga watan Mayun nan.