Jagora: Fitowar Mutane A Zabe Kare Karfi Da Kwarjinin Iran Ne.
Jagoran Juyin musulunci na Iran Ayatullahil-Uzmah Sayyid Ali Khamnei ya ce; Fitowar mutane a zabe, tana nufin nuna karfi da kuma kwarjinin Iran.
Jagoran Juyin musulunci na Iran Ayatullahil-Uzmah Sayyid Ali Khamnei ya ce; Fitowar mutane a zabe, yana nufin nuna karfi da kuma kwarjinin Iran.
Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya ci gaba da cewa; Ba abu ne mai muhimmancin ba wanda zai ci zabe, mai muhimmanci shi ne koma wanene ya tabbatar da cewa za a kare musulunci da kuma tsarin jamhuriyar musulunci."
Jagoran juyin musulunci na Iran wanda ya gana da malaman makarantu a yau lahadi, ya ce; Abinda ya ke takawa makiya birki, shi ne tsoron al'ummar kasa daya da adadinsu ya kai miliyan 80."
A halin da ake ciki a yanzu dai, yan takarar shugabancin kasa 6 suna ci gaba da yin yakin neman zabe.