Yau 'Yan Takarar Shugabancin Iran Ke Muhawara Ta Uku Kuma Ta Karshe
Yan takarar shugabancin kasar Iran su shida za su gudanar da muhawara talabijin karo na uku kuma na karshe a wannan Juma'a.
'Yan takarar 6 wato Hassan Rauhani, Ibrahim Ra'isi, Mustafa Agha Mir salim, Muhammad Bakir Qalibaf, Mustafa Hashimi Taba, Ishaq Jihagiri, dukkaninsu na hallara dakin tafka muhawarar da ke cikin babban ginin hukumar radiyo da ta talabijin ta kasa da ke Tehran.
Za'a fara fara muhawarar ce daga karfe 4:30 na yamma agogon Tehran, wato karfe 12:00 na rana agogon GMT.
Dukkanin 'yan takarar dai za su gabatar da bayanai dangane da shirye-shiryen da suke da su idan sun samu nasarar lashe zaben shugabancin kasar na ranar 19 ga watan Mayun nan, haka nan kuma za su amsa tambayoyi daga sauran abokan takararsu.