'Yan Takarar Zaben Shugaban Kasar Iran Sun Tafka Muhawarar Karshe
'Yan takara shugabancin kasa a Jamhuriya Musulinci ta Iran sun tafka muhawara talabijin ta uku kuma ta karshe a wannan Juma'a.
A muhawarar da aka watsa kai tsaye a mayan gidajen talabijin din kasar a kusan awowi uku, ko wanne daga cikin 'yan takaran guda shida ya bayyana manufofinsa da kuma kare siyasarsa a fagage da dama da kuma amsa tambayoyi daga abokan hammaya.
Daga cikin yan takara dai da akwai shugaban mai barin gado Hassan Ruhani, sauran kuma sun hada da Ibrahim Ra'isi, Mustafa Agha Mir salim, Muhammad Bakir Qalibaf, Mustafa Hashimi Taba da Ishaq Jihagiri.
Muhawarar dai tayi zafi sosai musamen tsakanin dan takara Hassan Ruhani da kuma yan hamayyarsa masu ganin cewa bai yiwa Iraniyawa komai ba duk da dagewa kasar takunkumi bayan cimma yarjejeniyar nukiliya.
A yayin da shi kuwa Ruhani ya soki manufofin nasu, kare gwamnatinsa ya yi da cewa tayi iyakar bakin kokarinta wajen inganta rayuwar al'ummar kasar.
Bayanai sun nuna cewa milyoyin jama'a ne a ciki da wajen kasar suka kalli muhawarar.
A ranar Juma'a mai zuwa ce wato 19 ga watan Mayu nan al'ummar kasar ta Iran zasu kada kuri'a a zaben shugabancin kasar karo na 12.