Iran Na Shirye Don Gudanar Da Zabubbuka
(last modified Sun, 14 May 2017 16:56:57 GMT )
May 14, 2017 16:56 UTC
  • Iran Na Shirye Don Gudanar Da Zabubbuka

Ministan harkokin gida a nan JMI ya bayyana cewa ma'aikatarsa a shirye take wajen ganin an gudar da zabubbuka masu inganci da adalci a duk fadin kasar a ranar jumma'a mai zuwa.

Abdurriza Rahmani Fadli ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da tashar television ta Channel 1 a nan Tehran, ya kuma kara da cewa sun sanyawa takardun zaben na jumma'a mai zuwa alamun gane ingancinsu har guda 14, wanda ba zai yu ba, ko kuma zai yi wuya wani ya yi magudin zabe da takardan jefa kuria.

Banda haka ministan ya kara da cewa a halin yanzu suna da sunayen dukkun iraniyawa kimani milion 80 a cikin komputocinsu, sannan mutum miliyon 56,015,000 suka cancanci zabe a wannan shekarar. Sai kuma cewa suk wanda bai da lambar danksa ba zai iya zabe ba.

A bangaren tsaro kuma Rahmani Fadli ya ce akwai jami'an tsaro 300,000 wadanda suke tsaron kan iyakokin kasar, sannan wasu 1560,000 kuma sune za su yi aikin a rumfunan zabe dubu 64 a duk fadin kasar. Banda haka wakilan majalisar kare kundin tsarin mulkin kasar kimani dubu 64 da kuma wakilan yantakara zsu kasance tare har zuwa lokacinda za'a bada sanarwan karshe na sakamakon zaben. Daga karshe ministan ya ce a bisa dokokin zaben JMI duk wanda yake da korafi kan sakamakon zaben yana da dama har zuwa kwanaki ukku don gabatar da korafinsa ga majalisar kare kundin tsarin mulkin kasar.

A Ranar jumma'a mai zuwa 19 ga watan mayu na wannan shekara ne za'a gudanar da zaben shugaban da na majalisun shoora na birane da larduna a duk fadin kasar Iran.