Iran : Qalibaf Ya Janye Daga Takara Zaben Shugaban kasa
(last modified Tue, 16 May 2017 05:44:40 GMT )
May 16, 2017 05:44 UTC
  • Magajin birnin Tehran, Mohammad Baqer Qalibaf
    Magajin birnin Tehran, Mohammad Baqer Qalibaf

Magajin birnin Tehran, Mohammad Baqer Qalibaf ya janye takararsa a zaben shugaban kasar Iran, wanda a yanzu ya rage 'yan takara biyar da zasu fafata a zaben.

A sanarwar da ya fitar Mista Qalibaf ya bukaci magoya bayansa dasu kadawa dan takara wanda ya kira da dan uwansa Ebrahim Raissi a babban zaben kasar dake tafe.

Wannan kuma a cewarsa don kare jama'a da kasar da kuma juyin juya halin musulinci.

 A yayin da rage kwana biyu a je zaben 'yan takara da suka rage sun hada da shugaban kasar mai barin gado Hassan Ruhani, sauran kuma sun hada da Ibrahim Ra'isi, Mustafa Agha Mir salim, Mustafa Hashimi Taba da Ishaq Jihagiri.

A ranar Juma'a mai zuwa ce wato 19 ga watan Mayu nan al'ummar kasar ta Iran zasu kada kuri'a a zaben shugabancin kasar karo na 12.