Ana Gab Da Kammala Yakin Neman Zabe A Iran
(last modified Wed, 17 May 2017 05:27:09 GMT )
May 17, 2017 05:27 UTC
  • Ana Gab Da Kammala Yakin Neman Zabe A Iran

A gobe ne da misalin karfe 8:00 agogon Iran wa'adin karshe na yakin neman zabe ke karewa a kasar Iran, inda a yau ne ake sa ran 'yan takarar za su gudanar da tarukan karshe tare da jama'a a yakin neman zaman zaben da suke yi.

A halin yanzu dai 'yan takara 4 ne suka yi saura daga cikin 'yan talarar 6 da ke neman kujerar shugabancin kasar Iran,a  zaben da za a gudanar a ranar Juma'a mai zuwa 20 ga wannan wata na Mayu 2017, bayan da 'yan takara biyu suka janye, wato Muhammad Qalibaf magajin garin birnin Tehran, wanda ya mara wa Sayyid Ibrahim Ra'isi baya, yayin da shi ma Ishak Jihangiri mataimakin shugaban kasa ya janye, inda shi kuma ya mara baya ga Hassan Rauhani, shugaban kasar da wa'adin mulkinsa na farko yake karewa, inda a halin yanzu 'yan takara 4 ne suka yi saura daga cikin 'yan takara 6.

Wannan dai shi ne karo na 12 da ake gudanar da zaben shugaban kasa a kasar Iran tun bayan juyin juya halin muslunci da aka yi a kasar a cikin shekara ta 1979, wanda ake gudanar da shi bisa tsari da kuma mahanga irin ta addinin ta addinin muslunci, bayan da al'ummar kasar suka kada kuri'ar farko ta raba gardama kan irin tsarin da suke so a gina kasar a kansa 'yan kwanaki bayan cin nasarar juyin juya hali, inda fiye da kashi 98 cikin dari na al'ummar kasar suka zabi tsarin musulunci.

Manyan 'yan takara da suka fi jan hankali a zaben a wannan karo dai su ne, Hassan Rauhani shugaban kasar da wa'adin mulkinsa na farko yake karewa, sai kuma Ibrahim Ra'isi, wanda mamba a majalisar zaben jagora a kasar, kamar yadda kuma mamba ne a babbar majalisar alkalai ta kasar, haka nan kuma shi ne shugaban cibiyar da ke kula da hubbaren Imam Ridha (AS) da ke birnin Mashhad.

A ranar Juma'ar da ta gabata ce dukkanin 'yan talarar suka tafka muhawara dangane da irin shirye-shiryen da suke da su idan suka samu nasarar lashe zabe, inda shugaba Rauhani ya fi mayar da hankali a kan batutuwa da suka shafi karfafa siyasar kasar a duniya, tare da bayyana hakan a matsayin babban abin da zai baiwa kasar dama wajen habbaka abubuwa da dama da suka shafi cikin gida, inda ya buga misali da cimma yarjejeniyar nukiliya da kasashen ketare, wanda hakan ya bayar da dama janye takunkumin da majalisar dinkin duniya tare da sauran manyan kasashen duniya suka kakaba wa Iran, wanda  cewarsa hakan ya bayar da dama ga Iran wajen ci gaba da fitar da danyen man fetur da isakar gas, tare da ci gaba da mu'amala da sauran kasashen duniya, tare da maido da mafi yawan kudadenta da aka rike su a kasashen ketare, da kuma bayar da dama ga masu saka hannayen jari daga kasashen ketare zuwa kasar, wanda a cewarsa hakan babbar dama ce da Iran za ta yi amfani da ita wajen kara karfafa ayyukan cikin gida da kyautata rayuwar jama'a, ta hanyar samar da ayyukan yi.

A nasa bangaren Ibrahim Ra'isi yana ganin mayar da hankali ga ayyukan cikin gida da karfafa jama'a wajen dogaro da kansu a cikin gida yafi muhimmanci al'ummar kasar, inda ya ce babban abin da yake da muhimamnci shi ne kasa ta tsaya a kan kafufunta tare da dogaro da jama'arta, tare da bunkasa ayyukan kere-kere da noma, ta yadda ko da takunkumi ko babu kasar ba za ta taba girgiza ba.

Ganin yadda dukkanin 'yan takara biyu Hassan rauhani da kuma Ibrahim Ra'isi suke da karfi da kuma magoyo baya a kasar, hakan ya sanya masu bin diddidin lamarin zaben kasar ta Iran suna yin taka tsantsan matuka wajen bayyana mahangarsu a kan wanda ake ganin zai lashe zaben a tsakaninsu, amma dai a ranar Juma'a mai zuwa, al'ummar kasar ta Iran za su raba gardama da katunan kuri'unsu.