Ana Daf Da Kada Kuri'a A Babban Zaben Iran
(last modified Thu, 18 May 2017 15:54:51 GMT )
May 18, 2017 15:54 UTC
  • Zaben Iran 2017
    Zaben Iran 2017

A yayin da ya rage 'yan sa'o'i kadan a fara kada kuri'a a babban zaben Jamhuriya musulinci ta Iran, ma'aikatar cikin gidan kasar ta ce ta shirya saf domin gudanar da zaben.

A gobe Juma'a ne al'ummar Iran ke kada kuri'a a zaben shugaban kasar gami dana wakilan jihohi da kuma na kauyuka. 

Ma'aikatar cikin gidan kasar ta sanar da cewa za'a bayyana sakamakon zaben daki-daki maimakon ta gabadaya da aka sanar tunda farko.

Da misalin karfe takwas na safiyar wannan Alhamis ce wato karfe (3h30 na dare ogogon GMT) aka rufe yakin neman zaben.

'Yan takara hudu ne dai zasu fafata a zaben shugaban kasar karo na 12 tun bayan juyin juya halin musulinci na kasar da suka hada da shugaba mai barin gado Hassan Rohani da Ebrahim Raïssi, da Mostafa Agha-Mirsalim, da kuma Mostafa Hashemi-Taba. 

Kafin hakan dai 'yan takara da suka hada da magajin birnin Tehran Mohammad-Baqer Qalibaf da kuma mataimakin shugaban kasar na farko Es'haq Jahangiri sun jange daga takarar zaben.