Takaitaccen Tarihin 'Yan Takarar Zaben Shugaban Kasar Iran Karo Na 12
(last modified Fri, 19 May 2017 03:56:34 GMT )
May 19, 2017 03:56 UTC
  • Takaitaccen Tarihin 'Yan Takarar Zaben Shugaban Kasar Iran Karo Na 12

Wannan dai takaitacce tarihin 'yan takaran zaben shugaban kasar Iran karo na 12 da kuma irin siyasa da ayyukan da suke son gudanarwa daidai da yadda cibiyoyin yakin neman zabensu suka fitar.

Da fari dai 'yan takara guda shida ne Ma'aikatar Cikin Gidan Iran din ta fitar a matsayin wadanda majalisar kula da kundin tsarin mulkin kasar ta Iran ta tantance da kuma sanar da su a matsayin wadanda aka amince musu su tsaya takarar a tsakanin sama da mutane dubu daya da dari shida da suka yi rajistar sunansu a matsayin wadanda suke son tsayawa takarar shugaban kasar a zaben da za a yi a ranar 19 ga watan Mayu 2017, wanda shi wannan zaben shi ne zaben shugaban kasa karo na 12 da za a gudanar tun bayan nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar Iran din a shekarar 1979.

To sai a ranakun karshe karshe, biyu daga cikin 'yan takaran wato magajin garin Tehran Muhammad Baqir Qalibaf da kuma mataimakin shugaban kasa Ishaq Jehangiri sun janye takarar na su da goya wa biyu daga cikin 'yan takaran wato Sayyid Ibrahim Ra'isi da kuma shugaba mai ci Hasan Ruhani baya.

Su dai wadannan 'yan takaran su ne:

  • Hasan Ruhani
  • Seyyed Ebrahim Raeisi
  • Mohammad-Baqer Qalibaf
  • Es'haq Jahangiri
  • Mostafa Aqa-Mirsalim
  • Mostafa Hashemi-Taba

Don haka a halin yanzu dai zaben zai kasance ne tsakanin wadannan 'yan takara guda hudu wato:

  • Hasan Ruhani
  • Seyyed Ebrahim Raeisi
  • Mostafa Aqa-Mirsalim
  • Mostafa Hashemi-Taba

Don haka ga kadan daga cikin tarihin na su:

(1). Dakta Hasan Ruhani.

Garin Haihuwa: Sorkheh, Lardin Semnan, da ke Arewa ta tsakiyar kasar Iran

Shekaru:  12 Nuwamban, 1948  (Shekaru 68)

Karatu Da Ilimi:

  • Makarantar Hauzar Qum (Fiqihu da Usul har zuwa 1979)
  • Jami'ar Tehran (Digirin farko da na biyu a bangaren shari'a a 1973 da kuma 1996)
  • Jami'ar Glasgow Caledonian University, Scotland (Digirin digirgir a shari'a a 2000)

Mukaman Da Ya Rike:

  • Dan majalisa a Majalisar Shawarar Musulunci daga 1984-2000
  • Mataimakin Kakakin majalisar shawarar Musulunci na farko daga 1992-2000
  • Babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran daga 1989-2005
  • Babban mai tattaunawa kan shirin nukiliyan Iran daga 2003-2005.
  • Memba a majalisar kwararru ta jagoranci ta Iran  daga 2007 har zuwa yanzu.
  • Babban sakataren kungiyar kasashen 'yan ba ruwanmu daga 2013-2016.
  • Shugaban kasar Iran na bakwai daga 2013 har zuwa yanzu.

Jam'iyya da Bangaren Da Yake:

  • Jam'iyyar Islamic Republic Party daga 1979–1987)
  • Kungiyar Malamai 'yan gwagwarmaya daga 1988 zuwa yanzu.
  • Jam'iyyar Moderation and Development Party daga 1999 zuwa yanzu.

Shirinsa Na Siyasa:

  • Siyasar tsaka tsaki cikin siyasar cikin gida da harkokin wajen.
  • Karfafa siyasar waje don kyautata alaka ta kasa da kasa
  • Kyautata yanayin tattalin arziki na cikin gidan.

(2). Hojjatoleslam Seyyed Ebrahim Raeisi

Garin Haihuwa: Birnin Mashhad, lardin Khorasan Razavi da ke arewa maso gabashin Iran.

Shekaru: 14 ga watan Disamban 1960 (shekara ta 56)

Karatu da Matsayin Ilimi:

  • Digiri a bangaren shari'a ta kasa da kasa.
  • Digirin digirgir a bangaren fikihu da usul daga Jami'ar Shahid Motahari.

Ayyuka Da Mukaman Da Ya Rike:

  • Mai shigar da kara a lardunan Karaj da Hamedan (1981)
  • Mataimakin mai shigar da kara na Tehran (1985)
  • Mai shigar da kara na Tehran (1989-1994)
  • Shugaban ofishin bincike na kasa (1994-2004)
  • Mataimakin shugaban hukumar shari'ar ta kasar Iran na farko (2004-2014)
  • Antoni Janar na kasar Iran (2014-2016)
  • Shugaban haramin Imam Ridha (a.s) daga shekara ta 2016 har ya zuwa yanzu.
  • Babban mai shigar da kara a kotun musamman ta malamai daga 2012.
  • Memba a majalisar kwararru ta jagoranci karo na 4 da na 5 daga 2006 zuwa yanzu.

Jam'iyya da Bangaren Da Yake:

  • Dan takarar jam'iyyar Popular Front of the Islamic Revolution Forces, hadin gwiwan masu tsaurin ra'ayi. 

Shirinsa Na Siyasa:

  • Karfafa tattalin arziki da kula da ita yadda ya dace.
  • Fada da rashin aikin yi da samar da hanyoyin aikin yi.
  • Alaka da dukkanin duniya in ban da HKI.
  • Tabbatar da hakkin 'yan kasa a aikace.

(3). Mostafa Aqa-Mirsalim

Garin Haihuwa: garin Tehran.

Age: 9 Yunin 1947 (Shekaru 69)

Karatu Da Ilimi:

  • Digiri a fannin Mechanics (1969)
  • Digiri a fannin Fluid Mechanics & Thermodynamics (both in 1971)

Ayyuka Da Mukaman Da Ya Rike:

  • Sufeto Janar na 'yan sanda (1980–1981)
  • Mai ba wa Ayatollah Seyyed Ali Khamenei shawara a lokacin yana shugaban kasa (1982-1989)
  • Mai ba wa shugaban kasa Ayatollah Akbar Hashemi Rafsanjani shawara (1989-1993)
  • Ministan al'adu da shiryarwa ta Musulunci (1993-1997)
  • Memba a majalisar fayyace maslahar tsarin Musulunci (tun daga 1997)

Jam'iyya Da Bangaren Da Yake:

  • Jam'iyar Islamic Coalition Party, (mai tsaurin ra'ayi).

Shirinsa Na Siyasa:

  • Karfafa bangaren masana'antu.
  • Karfafa bangaren kayayyakin da ake fita da su waje da masana'antun da suke haka.
  • Samar da guraban aikin yi ga matasa da wadanda suka yi karatu.
  • Kara irin abubuwan jin dadin al'umma da kuma fada da rashin aikin yi.
  • Karfafa abubuwan jin dadin al'umma. 
  • Kara kyautata hanyoyin sufuri da tafiye-tafiyen al'umma.

(4). Mostafa Hashemi-Taba

Garin Haihuwa: Lardin Isfahan, da ke tsakiyar Iran. 

Shekaru: 22 ga watan Mayu 1946, (shekaru 70). 

Karatu Da Ilimi:

  • Digiri a bangaren Textile Engineering a Jami'ar Fasaha ta Amir Kabir da ke Tehran.

Ayyuka Da Mukaman Da Ya Rike:

  • Ministan masana'antu (1981-1982)
  • Shugaban kwamitin Olympics na Iran (1986-1988)
  • Mataimakin shugaban kasa kuma hukumar motsa jiki ta Iran (1994-2001)
  • Mai ba wa ministan matasa da wasanni shawara (2014)
  • Dan takaran shugaban kasa a zaben shekara ta 2005.

Jam'iyya da Bangaren Da Yake:

  • Bangaren masu sassaucin ra'ayi.

Shirinsa Na Siyasa:

  • Kiyaye mutumci da matsayin Iran a yankin da take.
  • Sabuntawa da kuma kyautata bangaren ayyukan gona.
  • Goyon bayan talakawa da kyautata rayuwarsu.
  • Samar da guraben aikin yi.

 

(5). Muhammad Baqir Qalibaf

Garin Haihuwa: Mashhad, Lardin Khorasan Razavi da ke arewa maso gabashin Iran.

Haihuwa Da Shekaru: 23, Augustan 1961 (Shekaru 55)

Karatu Da Ilimi:

  • Jami'ar Tehran  inda ya sami digirin farko a fagen siyasa.
  • Jami'ar Tarbiat Modarres inda ya sami digiri na biyu da kuma na digirgir a fagen siyasar.

Ayyuka da Mukaman Da Ya Rike:

  • Kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci lokacin Iran-Iraq (1982-1988).
  • Kwamandan dakarun IRGC din na sansanin Khatam-al Anbiya (1984)
  • Kwamandan sojojin sama na dakarun IRGC din (1997-2000).
  • Sufeto Janar na 'yan sandan Iran (2000- 2005)
  • Shugaban kwamitin fada da fasa kwabrin kayayyaki da kudade (2004)
  • Dan takaran shugaban kasa a zaben shekara ta 2005 bangaren masu tsaurin ra'ayi.
  • Magajin garin Tehran daga shekara ta 2005 zuwa yanzu.
  • Dan takaran shugaban kasa a  2013.

Jam'iyya da Bangaren Da Yake:

  • Dan takarar jam'iyyar Popular Front of the Islamic Revolution Forces, hadin gwiwan masu tsaurin ra'ayi. 

Shirinsa Na Siyasa:

  • Karfafa da kuma kara kudaden shiga na kasa.
  • Samar da damar aikin yi.
  • Sabunta tsarin haraji na kasa.
  • Samar da tsari na gaggawa wajen kyautata yanayin tattalin arziki da rayuwar talakawa.

 

(5). Ishaq Jihangiri

Garin Haihuwa: Garinin Sirjan na lardin Kerman, da ke kudu maso gabashin Iran

Age: 10 Janairun 1957 (shekaru 60)

Karatu da Ilimi:
•    Digiri a bangaren ilimi kimiyyar lissafi (Physics) a jami'ar Shahid Bahonar da ke garin Kerman.
•    Digiri a fannin handasar masana'antu daga Jami'ar fasaha ta Sharif da ke Tehran.
•    Digirin digirgir a fannin handasar masana'antu daga Jami'ar Azad ta Musulunci a Tehran.


Ayyuka Da Mukaman Da Ya Rike:


•    Shugaban sashin aikin gona na kungiyar Jihadin Aikin Gona ta Iran na Lardin Kerman (1982)
•    Memba a majalisar shawarar Musulunci ta Iran karo 2 da 3 (1984-1992).
•    Gwamnan Esfahan (1992-1997)
•    Ministan tama da karafa (1997-2000)
•    Ministan masana'antu da tama (2000-2005)
•    Mataimakin shugaban kasa tun daga 2013.


Jam'iyya Da Bangaren Da Yake:


•    Jam'iyyar Executives of Construction Party, (masu sassaucin ra'ayi)

Shirinsa Na Siyasa:
•    Karfafa hadin kai na kasa.
•    Samar da guraben aiki miliyan guda.
•    Karfafa alaka ta kasa da kasa da karfafa matsayin Iran a duniya.
•    Magance kalubalen na tattalin arziki.