Yadda Iraniyawa Suka Nuna Da'a Da Kishin Kasa A Yayin Zabe
(last modified Sat, 20 May 2017 05:17:47 GMT )
May 20, 2017 05:17 UTC
  • Zaben na wannan karo ya samu karbuwa da gagarimin rinjaye
    Zaben na wannan karo ya samu karbuwa da gagarimin rinjaye

A yayin da al'ummar Iran ke dakon sakamakon zaben da aka kada kuri'arsa a jiya Juma'a, wani batu da ya dau hankalin duniya shi ne yadda Iraniyawan suka nuna da'a da kishin kasa a zaben.

Babu shakka yadda milyoyin al'ummar Iran suka fito don kada kuri''a a zaben shugaban kasar gami da na wakilan jihohi da na kauyuka ya zamo abun bada misali da yadda 'yan kasar suka karbi kiran magabatansu a zaben don baiwa marada kunya.

Sakamakon yadda al'ummar ta Iran suka fito ya cilasta ma'aikatar cikin gidan kasar ta tsawaita lokacin rufe mazabu har zuwa karfe 12 na dare, kasancewar har zuwa karfe takwas agogon GMT da aka tsara rufe mazabun akwai layin jama'a dake jira don kada tasu kuri'a.

kafofin yada labarai da dama sun rawaito cewa a cikin awawi 12 na zaben mutane miliyan talatin ne bisa miliyan 56 da dan kai, da suka tantanci kada kuri'a sun riga sunyi zabe.

Wasu iyalai na kada kuria'a a zaben Iran 2017

 

Alkalumen da ma'aikatar cikin gidan kasar ta fitar sun nuna cewa zaben na nya ya samu karbuwa da kashi 70% fiye da yadda aka saba gani a shekraun baya.

Mutumin farko da ya kada kuri'a a zaben na jiya shi ne jagoran juyin halin musulinci na Kasar Ayatollah Sayyid Ali Khamenei, wanda bayan hakan ya yi kira ga al'ummar kasar dasu hanzarta su kada kuri'arsu tunda saurin lokaci.

Jagoran addinin Islama na Iran lokacin da yake kada kuri'arsa 

 

Bayan hakan kuma an nuno sauren manyan , maluman kasar da suma suka kada kuria'a.

Su ma yan takara dake fafatawa a zaben sunyi kira ga al'ummar kasar dasu fito domin kada kuri'a.

Kira ga 'yan kasar don fitowa dafifi domin kada kuria'a shi ne mayan jami'an kasar da yan takara suka fi ba karfi wanda a cewarsu shi ne babban fatansu kasancewar hakan yana kara nuna yadda al'ummar kasar keda kishin kasa.

Dan takara Dr Hassan Rohani wanda ya kada tasa kuri'a a Tehran babban birnin kasar ya fadawa manema labarai cewa ''fitowar al'ummar kwansu da kwarkwatarsu lamari ne dake kara karfin da kasar keda da kuma tsaronta''

Shi kuwa a nasa bangare dan takara Ebarhim Ra'isi wanda ake ganin shi ne babban abokin hammaya na Ruhani ya yi kira ga al'ummar kasar dasu mutunta sakamakon zaben, duk da cewa shi ma Ruhani ya yi irin wannan kiran.

Sakamakon farko-farko ya nuna shugaba mai barin gado Hassan Rohani kan gaba da tazara kuri'u sama da milyan hudu

 

Tuni dai aka fara fitar da sakamakon zaben wanda za'a dinga bayyanawa daki-daki, inda dan takara Hassan Ruhani ke kan gaba da kashi 56% yayin Ibrahim Ra'isi ke biye masa da kashi 38%.

Ana kuma sa ran bayyana sakamakon zaben na dindin-din zuwa gobe Lahadi.

Mayan kalubalen dake gaban wanda aka zaba, bai wuce batun farfado da tattalin arzikin kasar ba, sai kuma batu na rashin aiki daya addabi matasan kasar da dama.