Ruhani:Kasar Iran Tana Bukatar Hulda Mai Mutunci Da Sauran Kasashen Duniya
Shugaban kasar Iran Dr Hassan Roohani ya bayyana cewa mutanen kasar Iran sun nunawa duniya cewa sun zabi tafarkin zaman lafiya da kuma mutunci, nesa da tashe tashen hankula a huldansu da sauran kasashen duniya.
Tashar television ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka ne a jawabinsa jim kadan bayan an tabbatar da cewa shi ne ya lashe zaben shugaban kasa wanda aka gudanar a nan jiya a duk fadin kasar.
Shugaban ya kara da cewa zaben da mutanen Iran suka yi a jiya ya tabbatarwa kasashe makobta da kuma yankin gabas ta tsakiya kan cewa tafarkin samar da zaman lafiya ita ce tafirkin democradia.
Banda haka shugaba Ruhani ya bayyana cewa fitowar mutanen kasar Iran duk tare da bambance bancen kabila da yanki da harshe suka yi zabe ya nuna cewa Iran kasa daya ce al-umma daya.
Zabebben shugaban kasar ya bukaci taimakon mutanen kasar gaba daya don aiwatar da alkawuran da ya yi masu a lokutan yakin neman zabe.
Ya kuma yi alkawarin zai kasashen shugaba ga dukkan mutanen Iran har tare da wadanad basu zabe shi ba.