Shugaban Iran Ya Meka Sakon Ta'aziyarsa Ga Takwaransa Na Afganistan
(last modified Fri, 02 Jun 2017 06:28:43 GMT )
Jun 02, 2017 06:28 UTC
  • Shugaban  Iran Ya Meka Sakon Ta'aziyarsa Ga Takwaransa Na Afganistan

Shugaban Kasar Iran Dakta Hasan Rauhani ya meka sakon ta'aziyar sa ga Takwaransa na kasar Afganistan da kuma iyalan wandanda harin ta'addancin da aka kai birnin Kabul ya ritsa da su.

A cikin wani sako da ya aike da shi ga takwaransa na kasar Afganistan, Shugaban Jumhoriyar musulinci ta Iran Dakta Hasan Rauhani ya yi alawadai da harin ta'addancin da aka kai birnin Kabul a wata mai alfarma na Ramadana sannan kuma ya meka t'aziyarsa ga ilahirin Al'ummar kasar Afganistan da kuma iyalan wadanda harin ya ritsa da su.

Dakta Rauhani ya ce wadanda suka kai wannan hari na ta'addanci a cikin watan Ramadana da kuma wadanda suka basu umarni da masu goyon bayansu , ba su da wata alaka da Addinin musulinci hasali ma ba su amfana da komai ba dangane da koyarwarsa.

A yayin da yake ishara kan tsayin daka da Al'ummar Iran suka yi  kusa da 'yan uwansu na Afganistan wajen yaki da ta'addanci, Shugaba Rauhani ya ce Jumhoriyar Musulinci ta Iran za ta ci gaba da kasancewa da Kasar Afganistan wajen yaki da ta'addanci.

Sama da mutane 80 ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu sama da 350 suka jikkata a sakamakon mumunan harin tashin bam da aka kai da safiyar  Laraba a birnin kabul na  kasar Afghanistan.