An Cabke Wasu Gungun 'Yan Ta'adda A Birnin Tehran
Jun 07, 2017 11:59 UTC
Babban Daraktan yaki da Ta'addanci na Ma'aikatar Leken Asirin Iran ya sanar da kame wasu gungun 'yan ta'adda da suka yi kokarin kai hare-haren ta'addanci a nan birnin Tehran a safiyar yau Laraba.
Kamfanin dillancin labaran Irna ya nakalto Jami'in ma'aikatar Leken asirin kasar ta Iran na cewa wasu gungun 'yan ta'adda biyu na daban sun yi kokarin kai hare-haren ta'addanci a Hubbaren Imam Khomeini (K.S) da Majalisar shawarar Musulunci ta kasar, inda jami'an tsaron kasar suka samu nasarar dakile harin.
Jami'in ya kara da cewa baya ga hakan Jami'an tsaro sun samu nasarar cabke wasu gungun 'yan ta'adda a birnin Tehran tun kafin su kaddamar da hare-haren ta'addanci a birnin.
Tags