Rasha Da Iran Za Su Kara Bunkasa Huldar Kasuwanci A Tsakaninsu
Wasu manyan jami'an gwamnatin kasar Rasha daga ma'aikatar harkokin kasuwanci ta kasar suna gudanar da wata ziyarar aiki a kasar Iran, domin bunkasa hada-hadar kasuwanci tsakanin Rasha da Iran.
A lokacin da suke ganawa da manyan jami'ai na ma'aikatar kula da harkokin kasuwanci ta kasar Iran a yau a birnin Tehran, jami'an gwamnatin kasar ta Rasha karkashin jagorancin Alexander Maksimov sun gabatar da wani shiri ga Iran kan batun kasuwanci.
Shirin na Rasha kuwa na da nufin mayar da wasu tashohin jiragen ruwa na Anzali da ke arewacin Iran da kuma tashar Maksimov da ke Rasha, su zama wurare na hada-hadar kasuwanci da babu haraji a tsakanin Rasha da Iran, shawarar da Iran da ta yi lalae marhabin da ita.