Kungiyar OPEC Na Kokarin Kyautata Farashin Mai
Kasashen Nigeria da Libya zasu halarci taron kungiyar OPEC Masu arzikin man Fetur da kuma wadanda basa cikin kungiyar na gaba wanda za'a gudanar a birnin Mosco na kasar Rasha. Kasashen dai suna son rage yawan man da suke haka don kyautata farashin man a duniya.
Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa kasashen biyu sun kara yawan man da suke haka bayan da an basu damar ci gaba da hakar man kamar yadda suka saba don matsalolin tsaron da suke fama da su a lokacin, amma a halin yanzu ana iya sanya su cikin wadanda zasu rage yawan man da suke haka don ganin farashin danyen man fetur yi kyau.
Ministan makamashi na kasar Rasha Alexander Novak ya fadawa kamfanin dillancin labaran reuters a birnin Istambul na kasar Turkia inda ya ke halattan taron taron masana'antu, ya na cewa ya tattauna da babban sakataren kungiyar OPEB Mohammad Barkinndo kan cewa nan da dan makonnu zasu kira wakilan kasashen biyu don tattayna batun.
Ministocin makamashi na kasashe shidda, membobi a kungiyar OPEC da kuma na wajen Opec zasu gudanar da taro a birnin Sient Pertersburg na kasar Rasha a ranar 24 ga watan yulin da muke ciki don tattauna batun kasuwar danyen man fetur a halin yanzu.
A cikin watan nuwamba mai zuwa ne ake saran ministocin makamashi na kasashen OPEC da na wajen OPEC zasu gudanar da taro don tattauna matakan da zasu dauna don kyautata farashin mai a shekara mai zuwa.