Makircin Masarautar Saudiyya Bai Cimma Nasara Ba A Zaman Kungiyar Kasashen Musulmi
Yunkurin mahukuntan Saudiyya na kokarin bata sunan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a zaman taron ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta O.I.C bai cimma nasara ba.
Babban daraktan bangaren kula da harkokin siyasa da tsaro a ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Ghulam Muhsin Dehqani ya bayyana cewa: Mahukuntan Saudiyya sun yi kokarin ganin zaman taron ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta O.I.C da aka gudanar a birnin Abidjan na kasar Ivory Coast ya yi suka kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran amma tsayin dakar jami'an Iran da wasu kasashen kungiyar ya rusa wannan makircin.
Kamar yadda mahalatta zaman taron suka fayyace cewa: Bukatar mahukuntan Saudiyya na aibanta kasar Iran ta yi hannun riga da manufofin kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta O.I.C.
Dehqani ya kara da cewa: Kullar makirce -makirce kan kasar Iran sune babban manufofin da aka cimma a zaman taron da ya hada mahukuntan Saudiyya da na Amurka a birnin Riyadh a ranar 21 ga watan Mayun wannan shekara, zaman taron da ya samu halattar kasashen musulmi da na Larabawa gami da shugaban kasar Amurka Donald Trump.