Martanin Iran Kan Sabbin Takukuman Amurka
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ta mayar da martani dangane da sabbin takunkuman da Amurka ta dora ma wasu kamfanoninta da kuma wasu jami'an kasar, dangane da shirin Iran na kera makamai masu linzami na ballastic.
A cikin bayanin da ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ta fitar a yammacin jiya, ta bayyana sabon takunkumin na Amurka da cewa ya saba wa dukkanin ka'idoji na kasa da kasa, domin kuwa babu wata doka ta duniya da ta haramta wa Iran kera makaman masu linzami domin kare kanta.
A jiya ne Amurka ta sanar da cewa ta kakaba sabbin takunkumai a kan wasu mutane da kamfanoni na kasar Iran da kuma wasu na China gami da kamfani guda na Turkiya, bisa hujjar cewa suna da alaka da shirin Iran na kera makamai masu linzami.
Bayanin ya ce saboda Amurka ta san cewa abin da ta yi ya saba wa da ma dukkanin dokoki na kasa da kasa, ta yi kokarin kare kanta da cewa, makaman da Iran take na Ballastic za su iya daukar kawunan makaman nukiliya, amma kuma a lokaci guda Amurka ta manta da cewa tana daya daga cikin bangarorin da suka rattaba hannu a kan yarjejeniyar shirin Iran na nukiliya, inda wannan yarjeniya da manyan kasashen duniya gami da majalisar dinkin duniya da kungiyar tarayyar turai da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya duk suka amince da ita, kan cewa shirin Iran ba na kera makaman nukiliya ba ne, wanda Trump da kansa daga bisani ya dawo ya yi ikirarin cewa zai ci gaba da mutunta wannan yarjejeniya.
A lokacin da yake zantawa da gidan talabijin na Aljazeera a jiya, ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewa, siyasar kasar Amurka musamman karkashin shugabancin Donald Trump cike take da tuka da warwara, domin kuwa abin da Amurka take ikirari na bin dokoki da kaidoji na kasa da kasa, yayin hannun riga da abin da take aikatawa.
A nasa bangaren babban hafsan hafsoshin sojin kasar Iran Janar Muhammad Baqiri ya bayyana cewa, babbar manufar Amurka ba makaman linzamin kasar Iran ba ce, manufar ita ce raunana tsarin da ke tafiyar da kasar wanda ya zama karfen kafa ga manufofin siyasar jari hujja ta Amurka a yankin gabas ta tsakiya. A kan haka ya ce; martanin da Iran za ta mayar shi ne kara inganta wadannan makamai, da kuma kara tsawon zangon da za su iya kaiwa, tare da karfafa rundunar Failaq Badr da ke gudanar da ayyukan soji a wajen Iran, wadanda suka hana Amurka da 'yan korenta na yankin gabas ta tsakiya cimma manufofinsu a Iraki da Syria.
A zaman da majalisar dokokin kasar Iran ta gudanar a jiya, ta kada kuri'a kan amincewa da daukar matakai na mayar da martani a kan Amurka kwatankwacin abin da ta yi, inda a hukuamnce Iran za ta fitar da sunayen jami'an da kuma kamfanonin Amurka da suke da alaka da ayyukan ta'addanci domin kakaba musu takunkumi.
Da dama daga cikin masana harkokin siyasar kasa da kasa suna ganin cewa, Amurka ta dauki wannan mataki ne a kan Iran domin huce haushinta a kan rawar da Iran ta taka wajen fatattakar 'yan ta'adda daga birnin Mosul na kasar Iraki, wadanda 'yan koren Amurka daga cikin larabawa suka kashe biliyoyin daloli wajen daukar nauyinsu, kamar yadda kuma hakan take faruwa a Syria, inda Iran ta zama karfen kafa Amurka da Isra'ila da 'yan korensu daga cikin larabawa wajen hana su cimma burinsu na wargaza wannan kasa kamar yadda suka shirya, kuma suke ta hankoron yin hakan tun kimanin shekaru 6 da suka gabata, kuma har yanzu ba su ci nasara ba.