Iran : Rohani, Ya Sha Rantsuwar Kama Aiki A Wa'adi Na Biyu
(last modified Sat, 05 Aug 2017 14:31:25 GMT )
Aug 05, 2017 14:31 UTC
  • Rohani ya sha ranstuwa kama aiki a wa\\\\\\\'adin mulki na biyu
    Rohani ya sha ranstuwa kama aiki a wa\\\\\\\'adin mulki na biyu

Zababen shugaban Jamhuriya muslinci ta Iran, Hassan Rohani ya yi rantsuwa kama aiki a wa'addin mulkinsa na biyu a yau Asabar.

Dakta Rohani, ya yi rantsuwar kama aiki a gaban majalisar dokokin kasar, a matsayinsa na shugaban kasar Iran na 12.

Shuwagabanni da wakilan gwamnatocin kasashe da dama ne suka halarci bikin a  birnin Tehran, daga cikinsu kuwa har da shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe.

Sauren wakilan kasashen sun hada dana Koriya ta Arewa, Irlande, Croatia, Hongrie, Lithuania, Portugal, Malaysia, Uganda, Saliyo, Tanzania, Swaziland Namibiya sai kuma babbar jami'ar diflomatsiyar kungiyar kasashen turai da wakilin shugaban mabiya darikar katolika, Paparoma Francis a daya bangare.

A watan Mayu da ya gabata ne Hassan Rohani ya lashe zaben shugabancin kasar ta Iran da kashi 57% na yawan kuri'un da aka kada.