Rauhani Ya Aike Sakon Taya Shugabannin Kasashen Musulmi Murnar Sallah
(last modified Fri, 01 Sep 2017 11:19:39 GMT )
Sep 01, 2017 11:19 UTC
  • Rauhani Ya Aike Sakon Taya Shugabannin Kasashen Musulmi Murnar Sallah

Shugaba Rauhani na kasar Iran ya aike da sakonnin zuwa ga shugabannin kasashen musulmi, inda yake taya su murnar sallah, da kuma yi musu fatan alkhairi tare da al'ummomin kasashensu.

Shafin yanar gizo na shugaban kasar Iran ya bayar da rahoton cewa, a cikin wasikar tasa zuwa ga shugabannin kasashen musulmi, shugaba Rauhani ya bayyana fatan ganin an samu zaman lafiya da fahimtar juna  atsakanin dukkanin al'ummar msuulmi, tare da kawo karshen tashe-tashin hankula da ake haifarwa a cikin kasashen musulmi da nufin raunana su.

Haka ann kuma shugaban ya yi ishara da halin da musulmi marassa rinjaye suke ciki a wasu kasashen, inda suke fuskantar zalunci da kisan kiyashi, inda yake bayyana hadin kan musulmi a matsayin hanya daya tilo ta kawo karshen duk wani zalunci da ake yi wa musulmi.

Daga karshe kuma ya yi fatan alkhari ga dukkanin mahajjata da suke gudanar da aikin hajji, da fatan Allah ya karbi ibadarsu, ya kuma mayar da kowa gida lafiya.