Sep 25, 2017 19:36 UTC

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Jawabin shugaban kasar Iran a zaman taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya karo na 72 a birnin New York na kasar Amurka ya fito da hakikanin fuskar siyasar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a yankin gabas ta tsakiya dama duniya baki daya.

A taron manema labarai da ya gudanar a yau Litinin: Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Bahroum Qasimi ya bayyana cewa: Matakin da Amurka ta dauka na kokarin cusa wa duniya kiyayya da Jamhuriyar Musulunci ta Iran tare da gabatar da zarge-zarge marassa tushe da kan gado kan kasar Iran bai yi nasara ba, sakamakon haka shugabannin duniya daban daban gami da wakilinsu suka dauki matakin ganawa da jami'an kasar Iran musamman shugaban kasar Dr Hasan Ruhani da ministan harkokin wajen kasar Muhammad Jawad Zarif.

Qasimi ya kara da cewa: Tun farkon bude zaman taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya zuwa yanzu jami'an kasar Iran sun gudanar da zaman tattaunawa da jami'an kasashen duniya da gudanar da taron manema labarai fiye da 42, kuma a halin yanzu haka akwai wasu zaman tattaunawan da zasu gudana tsakanin jami'an na Iran karkashin jagorancin ministan harkokin wajen kasar da wasu shugabannin duniya gami da wakilinsu a birnin na New York na kasar Amurka.

Tags