Oct 14, 2017 19:14 UTC
  • Jakadan Nigeriya A Kasar Iran Ya Mika Takardar Kama Aiki Ga Shugaban Kasar Dr Hasan Ruhani

Shugaban kasar Iran ya jaddada aniyar kasarsa ta bunkasa alaka da taimakekkeniya tsakaninta da kasar Nigeriya.

A jawabinsa a bikin karbar takardar kama aiki daga sabon jakadan kasar Nigeriya a Jamhuriyar Musulunci ta Iran Alh. Hamza Ibrahim Tsiga a yau Asabar: Shugaban kasar Iran Dr Hasan Ruhani ya jaddada bukatar matsa kaimi a tsakanin mahukuntan Iran da Nigeriya wajen hanzarta aiwatar da tarin yarjejeniyar da aka cimma tsakaninsu; Yana mai bayyana cewa: Dole ne kasashen biyu su dauki matakin bunkasa alakarsu a bangarori da dama saboda tarin arzikin karkashin kasa da masana'antu da Allah ya huwace musu.

Har ila yau Dr Hasan Ruhani ya jaddada shirin kasarsa na gudanar da ayyuka a tarayyar Nigeriya a fuskar kimiya da fasaha da suka hada da samar da hanyoyi, makamashi, wutan lantarki tare da bunkasa harkar al'adu, jami'o'i, tattalin arziki da sauransu. Haka nan Shugaba Ruhani ya bayyana wajabcin samun hadin kai da gudanar da aiki tare tsakanin Nigeriya da Iran a kungiyoyin kasa da kasa musamman a fagen yaki da ayyukan ta'addanci sakamakon yadda ta'addanci ya zame hatsari ga dukkanin duniya.

A nashi bangaren Jakadan Nigeriya a Iran Alh. Hamza Ibrahim Tsiga ya jaddada wajabcin bunkasa alaka da taimakekeniya a bangarori da dama a tsakanin kasashen Nigeriya da Iran, kamar yaddada ya jaddada aniyarsa ta yin aiki tukuru domin ganin an cimma wannan manufa. 

 

Tags