Sheikh Siddiqi: Makiya Sun Ci Kasa A Dukkanin Makirce-Makircensu Kan Iran
Wanda ya jagoranci sallar Juma'ar birnin Tehran, Hujjatul Islam wal Muslimin Kazim Siddiqi ya bayyana cewar makiyan al'ummar Iran suna ci gaba da shan kashi a kan makirce-makircen da suke kullawa wa Iran, sai dai kuma duk da haka suna ci gaba da kokari wajen rarraba kan al'ummar wanda ya ce shi ma ba za su yi nasara ba.
Hujjatul Islam Siddiqi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da hudubar sallar Juma'a a masallacin Juma'a na Tehran a yau din nan inda ya ce makiyan al'ummar Iran sun gaza a makirce-makircen da suke kulla wa Iran tun bayan nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar, yana mai cewa al'ummar Iran za su ci gaba da riko da kuma ba da kariya ga juyin na su.
Yayin da ya koma kan batun makamai masu linzami na Iran da kuma dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar da Amurka take ci gaba da magana a kansu, Sheikh Siddiqin ya ce har ya zuwa yanzu makiyan ba su fahimci al'ummar Iran ba, yana mai cewa dakarun kare juyin juya halin Musuluncin wani bangare ne na al'ummar Iran da ba za taba bari wani abu ya same su ba.
Yayin da yake magana kan yarjejeniyar nukiluya da Iran ta cimma da manyan kasashen duniya kuwa wanda a halin yanzu shugaban Amurka Donald Trump yake magana zai yi watsi da ita, Hujjatul Islam Siddiqi ya ce wadannan abubuwa da Amurka take yi dai na dada tabbatar da abin da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya sha fada ne cewa Amurka dai ba abar yarda ba ce.